Premier : Newcastle ta ci Stoke City

newcastle stoke
Image caption Necastle ta yi nasara a kan Stoke City

Kungiyar Newcastle ta taso daga baya ta yi nasara a kan Stoke da ci 2-1 a gasar Premier.

Bayan wasan kashin farko da bai yi wani armashi ba a minti na 67 Jonathan Walters ya ci wa Stoke kwallonta daya a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Amma kuma rashin kulawar 'yan wasan baya na Stoke ya baiwa Yohan Cabaye damar rama kwallon a minti na 72.

Can kuma a daidai karshen wasan a minti na 90 Cisse ya je fa kwallo ta biyu ragar 'yan Stoke.

Yanzu Stoke City ita ce ta 11 a teburin Premier da maki 33 a wasanni 29 da bambancin kwallaye 8.

Ita kuwa kungiyar Newcastle ta dago sama zuwa matsayi na 13 ita ma da maki 33 wasa 29 amma kuma bambancin kwallaye 10.

Liverpool da Tottenham

Liverpool ta fardfado da fatanta na shiga cikin kungiyoyi hudu da ke kan gaba a Premier inda ta samu nasara a kan Tottenham da ci 3-2.

Suarez ne ya fara ci wa Liverpool a minti na 21 amma Vertonghen ya rama a minti na 45, kuma ya sake ci bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 53.

Downing ya rama wa Liverpool a minti na 66 sannan kuma a Gerrard kara ta uku a bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanareti).

Yanzu maki bakwai ne tsakanin Chelsea ta hudu a tebur din Premier mai maki 52 ko da ike dai Chelsean ta na da kwatan wasa daya.

Manchester United ta na ta daya da maki 71 da wasa 28, Manchester City na matsayi na biyu da maki 59 wasa 28 Tottenham kuwa ta na ta uku da maki 54 amma wasa 29.