Rooney zai samu sabon kwantiragi - Ferguson

wayne rooney da ferguson
Image caption Ferguson ya ce '' za mu sabunta kwantiragin Rooney''

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce Za a sabunta kwantiragin Wayne Rooney a kungiyar.

A makon da ya wuce ne Ferguson ya bada tabbacin cewa kungiyar ba za ta bar Rooney ya tafi ba a karshen kakar wasannin bana ba.

Ya tabbatar da hakan ne kuwa duk da rashin sa shi a farkon wasan klub din da Real Madrid.

Kwantiragin Rooney dan shekara 27 na yanzu zai kare ne a 2015.

Ferguson ya ce ''babu wata matsala game da kwatiragin dan wasan za a tattauna a kai idan lokaci ya yi.''

Ya ce '' ba za mu bar 'yan wasa masu kyau su tafi ba.''

Sai dai kuma tsohon kocin Arsenal da Tottenham George Graham ya na ganin United za ta rage wa Rooney armashin kwantiragin nasa.

A don haka ya ke gani zai bar kungiyar a karshen kakar bana.

Graham ya ce '' shekaru biyu ne aka saba kulla kwantiragi akai. Na tabbata kungiyar za ta bashi sabon

kwantiragi amma kudin ba zai kai na yanzu ba.

''Ina ganin Rooney ba zai ci gaba da zama a United ba amma kuma kungiyoyin da za su iya sayen shi ba su da yawa.''

Karin bayani