David Beckham ya fi kowane dan kwallo kudi

David Beckham
Image caption Editan kafar yada labaran da ta fitar da jerin 'yan wasan Amar Singh, ya ce 'yan kwallon ba wai kawai 'yan wasa ba ne, suma wasu manyan hajoji ne

Dan wasan kulob din Faransa na Saint Germain, wato David Beckham ya fi kowane dan wasa wadata a duniya, inda ya mallaki wuri na gurar wuri fam miliyan 175.

Yayin da Lionel Messi na Barcelona ke biye da shi, sai kuma Cristiano Ronaldo na kulob din Real Madrid.

David Beckham ne ya sha gaba a jerin ‘yan wasa mafi wadata a duniya na shekarar 2013.

Beckham ya fi Messi kudi da sama da fam miliyan 59, wato Messi na da fam miliyan 115, inda shi kuma Cristiano Ronaldo ke da fam miliyan 112.

Duk da cewa Real Madrid bata sa shi buga wasa sosai, Kaka shi ne na hudu a jerin ‘yan kwallon da suka fi kowa wadata, inda yake da sama da fam miliyan 66, sai na biyar dinsu Ronaldinho, wanda ke da fam miliyan 63.

An kiyasta arzikin kowane dan wasan ne bisa la’akari da albashinsa da kwantiraginsa da kadarorinsa da kuma harkokin kasuwancinsa.

Beckham ya zama na farko duk da cewa ba zai karbi ko kwabo a matsayin albashi ba daga kulob din St. Germain, tun da ya bada albashinsa sadaka ga yara marasa galihu.