Bolt ya samu lambar yabo ta Laureus

usain bolt
Image caption Usain Bolt ya sha alwashin sake kare kambunansa a 2016

Zakaran tseren mita 100 da kuma 200 na wasan Olympics Usain Bolt ya samu lambar gwarzon dan wasa na shekara ta 2013 ta Laureaus.

Wannan shi ne karo na uku da Usain Bolt ya ke samun lambar yabon ta gwarzayen 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsallen ta Laureus.

Ya yi nasarar ne saboda kare kambunsa na tseren mita 100 da 200 a wasan Olympics na London.

Kafin gasar ta London Bolt shi ne daman ya ke rike da kambun tseren biyu da ya samu a gasar Olypics ta Beijin.

Dan tseren ya sake samun lambar yabon ta Laureus ce a wannan karon bayan da a shekarar 2009 da 2010 ya karbe ta.

Usain Bolt ya yi alkawarin kara kare dukkanin kambunansa a gasar Olympics ta 2016 a Rio.