Sai Liverpool ta zage damtse - Gerrard

Steven Gerrard
Image caption A ranar 31 ga watan Maris ne kulob din zai kara da Aston Villa

Kyaftin din 'yan wasan Liverpool, Steven Gerrard ya ce sai kulob din ya zage dantse a kakar wasannin da ake ciki, kafin ya samu shiga Champions league a badi.

A yanzu dai kulob din shi ne na shida a jerin kulob-kulob a gasar premier league, inda ya ke da maki bakwai a bayan Chelsea, wacce ita ce kulob ta hudu, yayin da ya rage saura wasanni tara a kammala gasar premier league.

"Ina ganin lokaci bai kure ba" Inji Gerrard

Ya kara da cewa "Sai mun yi aiki tukuru, idan muna son mu samu kanmu a gaba-gaba. Muna harin shiga kulob biyar na farko, bari dai mu ga abin da zai faru a manyan wasannin da bamu da iko da su. "

"Watakila wasu daga kulob din da ke gabanmu su yiwo kasa, abin da kawai za mu iya yi shi ne zage dantse wajen yadda muke wasa, domin ganin mun kammala da karfinmu. " Inji Kyaftin din.

Kulob din da ake wa lakabi da Reds a turance, ya lashe wasanni uku da yayi na baya-bayan nan a gasar, ciki har da wanda ya doke Tottenham da ci 3-2 a ranar Lahadin da ta wuce.