Arsenal za ta iya doke Munich - Wenger

Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger
Image caption Arsenal ita ce kulob ta biyar a gasar Premier, kuma bata cikin kulob-kulob din da suka samu shiga gasar Zakarun Turai

Manajan kulob din Arsenal, Arsene Wenger ya ce kulob din zai iya lallasa Bayern Munich, a karawar da za su yi ranar Laraba kuma, Arsenal ta samu shiga zagayen gaf da na kusa da na karshe.

Wenger yace kulob din zai iya rama dokensu da Munich ta yi da ci 3 da daya.

Sai dai rashin mai tsaron gida Wojciech Szczesny da Jack Wilshere da Bacary Sanga, zai sa wannan buri na Wenger ya zama mai wuya.

"Mun san zai yi wuya, amma ba abu bane da za a ce ba zai yiwu ba." Inji manajan.

"Kuma hanya daya ta cimma hakan, ita ce mu sa kanmu cewa za mu iya, kuma haka za mu yi. Mu shiga wasan muna sa ran cewa za a doke mu, abu ne da ba za mu taba yarda da shi ba." A cewar Wenger.

Amma kulob din Munich na Jamus bai yarda an zura masa kwallaye uku a raga ba, a takaledar da ya dauki bakuncinsu, tun lokacin da Inter milan ta bi su har gida ta lallasa su, shekaru biyu da suka wuce.

Sai dai Wenger ya yi amanna hakan ba zai basu tsoro ba.