An sa ranar Chelsea da Man U

chelsea Man united
Image caption Chelsea da Man United za su sake fafatawa

An sanya ranar 1 ga watan Aprilu ta zama ranar da za a sake fafatawa tsakanin Chelsea da Manchester United a wasan Kofin FA.

A karawarsu ta farko ta wasan gab da na kusa da karshe a gidan Man United Old Trafford ranar Lahadi sun tashi ne 2-2.

Lokacin wasannin sada zumunta tsakanin kasashe daga ranar 18 zuwa 27 na watan Maris da kuma wasannin kofin Europa na Chelsea su suka sa matsalar tsaida sabuwar ranar. Yanzu an tsaida ranar 1 ga watan na Aprilu ne bayan da Chelsea ta zabi ranar 30 ga watan Maris domin wasanta na Premier da Southampton.

A lokacin ita kuma kungiyar Manchester United za ta je wasa da Sunderland.

Duk kungiyar da ta yi nasara tsakanin Chelsea da United bayan makwanni biyu za ta hadu da Manchester City a wasan kusa da na karshe a wembley.