FIFA ta gargadi Tanzania

tanzania flag
Image caption Tanzani ba ta taba zuwa gasar Kofin Duniya ba

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta gargadi hukumomin kasar Tanzania kan tsoma baki da gwamnati ke yi a hukumar kwalln kasar.

Hukumar ta FIFA ta na kuma shirin tura wata tawagar jami'anta domin duba batun katsalandan din dangane da zaben hukumar da zarar ta tabbatar da tsoma bakin na gwamnati.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa gwamnatin ta sanar wa hukumar kwallon ta Tanzania sabbin dokokinta sun saba ka'ida a don haka ta umarce ta ta yi amfani da tsoffin wajen gudanar da zabukanta dake tafe.

Ka'idojin FIFA dai sun bukaci hukumomin kwallon kasashe da kada su kasance karkashin ikon gwamnatocinsu kuma ta kan dakatar da wadanda suka saba ka'idojin.

Idan FIFA ta dakatar da Tanzania hakan zai sa a fitar da ita daga gasar neman zuwa wasan Kofin Duniya na 2014 kuma kungiyoyin wasan kasar su ma za a fitar da su daga wasannin nahiyar.

Tanzania wadda ba ta taba zuwa wasan Kofin Duniya ba ita ce ta biyu a rukuni na uku, Group C da maki 3 inda ta ke ta biyu a bayan Ivory Coast ta daya da bambancin maki daya.