Blatter : Gasar Euro ba za tai armashi ba

sepp blatter
Image caption Sepp Blatter na shirin ritaya a 2015

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA Sepp Blatter ya ce gasar Kofin kasashen Turai ta 2020 ba za ta yi armashi ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne saboda shirin hukumar kwallon Turai Uefa na gudanar da gasar a kasashe dabam dabam.

Blatter ya ce ''a kasa daya ya kamata a gudanar da gasa ta haka gasa ke yin armashi kuma kasa ta yi fice.''

A watan Janairu ne Uefa ta sanar cewa za a gudanar da wasannin gasar a birane 13 kuma kowannensu a kasa dabam.

Amma kuma a guda daya za a yi wasannin kusa da na karshe da kuma na karshe.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai Michel Platini na goyon bayan birnin Istanbul ya samu damar karbar bakuncin wasan karshen idan babban birnin na Turkiyya ya rasa damar wasan Olympics.

Blatter wanda ya ke shugabancin FIFA tun 1998 na shirin sauka a 2015 idan hukumar ta bunkasa.

Kuma ana ganin tsohon dan wasan Faransa Platini ne zai gaje shi.