Zakarun Turai: PSG za ta kara da Barca

Zakarun Turai
Image caption Za a yi wasannin farko a ranakun 2 ko 3 ga watan Afrilu sannan a yi zagaye na biyu a ranakun 9 ko 10 ga Afrilu

Barcelona wacce ta taba lashe kofin sau hudu za ta kara ne da Paris Saint-Germain a wasan dab da na kusa da na karshe (quater-finals) na gasar cin kofin zakarun Turai.

Jose Mourinho da tawagarsa ta Real Madrid za su kece raini ne da Galatasarary, inda zai hadu da tsohon dan wasansa Didier Drogba.

Yayin da Bayern Munich za ta kara da Juventus, sai Malaga da za ta fafata da Borussia Dortmund.

Za a yi wasannin farko a ranakun 2 ko 3 ga watan Afrilu sannan a yi zagaye na biyu a ranakun 9 ko 10 ga Afrilu.

Ga yadda wasannin za su kasance:

Malaga da Borussia Dortmund

Real Madrid da Galatasaray

Paris Saint Germain da Barcelona

Bayern Munich da Juventus

Karin bayani