Dibaba ba za ta yi tseren Landan ba

tirunesh dibaba
Image caption Tirunesh Dibaba ta dauki lambar tagulla bayan ta zinare a Landan

'Yar tseren dake rike da kambun gasar gudun famfalaki na mita 10,000 na Olympics Tirunesh Dibaba ta janye daga gasar da za a yi a Landan.

'Yar tseren mai shekara 27 'yar kasar Habasha (Ethiopia) wadda ta kare kambunta a wasan Olympic na Landan na 2012 za ta shiga gasar da za a yi ne a Landan ranar 21 ga watan Aprilu.

Amma a yanzu ta fasa shiga gasar ta gudun famfalakin ta Landan saboda raunin dake damunta a kafa.

Dibaba ta ce ''kara nisan tseren da nake yi ne ke sa ciwo na na da ya ke ta kara taso min amma ina fatan shiga gasata ta farko a Landan a shekara mai zuwa.