Tottenham ta tsallake rijiya da baya

tottenham da inter milan
Image caption Tottenham ta shiga wasan gab da na kusa da karshe

Tottenham ta tsallake rijiya da baya a gasar Kofin Europa inda ta tashi da Inter Milan 4-4 a karawa biyu.

A wasansu na farko Tottenham a gida ta ci Inter 3-0.

A wasansu na biyu ranar Alhamis Inter ta ci su 4-1.

Sanadiyyar kwallo 1 da suka ci sun samu galaba a kan Inter Milan.

Wasannin tsakanin kungiyoyi 16 ne zagaye na biyu.

Bayan wasan za a samu kungiyoyi 8 da za su shiga wasan gab da na kusa da karshe.

Sakamakon wasannin

Rubin Kazan' 2 - 0 Levante

Zenit 1 - 0 Basel

Internazionale 4 - 1 Tottenham Hotspur (4-4)

Fenerbahçe 1 - 1 Viktoria Plzeň

Bordeaux 2 - 3 Benfica

Newcastle United 1 - 0 Anzhi

Lazio 3 - 1 Stuttgart

Chelsea 3- 1 Steaua Bucureşti