Sai mun tashi tsaye - Wenger

Arsene Wenger
Image caption Shekaru 17 kenan rabon da ayi zagayen dab da na kusa da na karshe ba tare da kulob din Ingila ba

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce yadda kungiyoyin gasar Premier suka kasa kaiwa zagayen dab da na kusa da na karshe a gasar zakarun Turai, ya nuna cewa "sai sun tashi tsaye".

Nasarar da Bayern Munich ta samu a kan Arsenal ranar Laraba ta nuna cewa babu kulob din Ingila da ya kai zagayen dab da na kusa da na karshe tun kakar wasanni ta 1995-96.

"Ba karamin koma-baya ba ne ga kwallon kafa a Ingila," a cewar Wenger.

"Mun amince cewa ragowar kungiyoyin Turai sun shiga gabanmu."

Zakarun Ingila Manchester City sun zo na karshe a rukuninsu, wanda ya hada da Real Madrid, Borussia Dortmund da kuma Ajax, bayan da suka kasa lashe wasa ko daya.

Chelsea, wacce ta doke Bayern Munich a wasan karshe na bara, su ma basu iya tsallake rukuninsu ba, yayin da Manchester United ta sha kashi a hannun Real Madrid.

Arsenal wacce ta sha kashi da ci 3-1 a wasan farko, ta doke Bayern Munich 2-0 a Jamus ranar Laraba sai dai an fitar da ita saboda yawan kwallaye bayan wasa gida da waje.

Karin bayani