Chelsea ta casa West Ham

chelsea da west ham
Image caption Chelsea ta matsa sama a gasar Premier

Kugiyar Chelsea ta samu tagomashin zuwa mataki na uku na gasar Premier da nasarar da ta samu a kan West Ham 2-0 a gidanta Stamford Bridge.

Kwallayen da Lampard da Hazard suka ci a minti na 19 da kuma 50 su suka ba Chelsean damar galaba a kan West Ham din wadda ke hamayya sosai da ita a Landan.

Kwallon da Lampard ya ci ita ce ta 200 da ya ke ci wa kungiyar kuma yanzu kwallaye biyu suka rage ya kaom bajintar da Bobby Tambling ya yi wa klub din na cin kwallaye.

Chelsea ta samu damar hawa mataki na ukun ne a teburin na Premier inda ta kawar da Tottenham wadda Fulham ta ci 1-0 a gida.

Yanzu maki 4 ne tsakanin Manchester City ta biyu da Chelsea ta uku a tebur da wasanni 29.

Yayin da Manchester United ta ci gaba da kasance wa ta daya da maki 74 a wasanni 29 da kuma bambancin kwallaye 38.