Sakamakon gasar Premier

tottenham fulham
Image caption Fulham ta kawo wa Tottenham cikas

A gasar Premier an yi wasanni hudu ne ranar Lahadi inda kungiyoyi uku suka yi nasara yayin da aka tashi kunnen doki a wasa daya.

Tottenham a gida ta yi rashin nasara a hannun Fulham da ci 1-0, Wigan a gidanta ta yi galaba a kan Newcastle 2-1 kamar yadda Chelsea a gida ta casa West Ham 2-0 yayin da Sunderland ta yi kunnen doki 1-1 da Norwich.

West Hoolahan ne ya ci wa Norwich kwallonta minti 26 da wasa sai kuma can a minti na 40 Gardner ya rama wa Sunderland da bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida (fanareti).

Wasa tsakanin Tottenham da Fulham Dimitar Berbatov ne ya ci tsohuwar kugiyar tasa Totteham a minti na 52.

Cin kwallon daya ya maida wa Tottenham din hannun agogo baya a kokarin da take na kammala gasar ta Premier a matsayi na hudu.

Duk da cewa klub din ne na hudu a Premier da maki 54 har yanzu amma bambancinsa da Arsenal ta biyar maki 4 kawai kuma Arsenal din na da wasa daya.

A karawar Wigan da Newcastle Jean Beausejour ne ya fara ci wa Wigan kwallon farko a minti na 18 sannan daga baya Davide Santon ya rama a minti na 72.

Can a minti na 90 ne kuma Arouna Kone ya ci wa Wigan kwallo ta biyu wadda ta kasance mai matukar muhimmanci ga kungiyar wadda take ta ukun karshe a Premier da maki 27 a wasanni 29.

Reading ita ce ta 19 da wasanni 30 da maki 23 kamar yadda QPR ta karshe take kuma dukkanninsu an jefa musu kwallaye 22.