Rio Ferdinand ya fasa bugawa Ingila

rio ferdinand
Image caption Rio Ferdinand sau 81 yana bugawa Ingila wasa

Dan wasan baya na Manchester United Rio Ferdinand ya janye daga shirin bugawa Ingila wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya da San Marino da kuma Montenegro.

An bayyyana hakan ne bayan ganawar da dan wasan mai shekaru 34 ya yi da kocin Ingila Roy Hodgson ranar Lahadi.

Roy Hodgson ya ce ''na ji takaicin cewa Ferdinand ba zai samu damar buga wasannin ba amma saboda ka'idojin kula da lafiyarsa da aka gindaya masa ne ba zai iya ba.''

Duk da janyewar a yayin ganawar tasu Ferdinand ya bayyana aniyarsa ta cigaba da yi wa Ingila wasa.

Yanzu za a dawo da dan wasan Tottenham Steven Caulker wanda da aka sanya shi cikin tawagar 'yan wasan Ingila 'yan kasa da shekara 21 ya shiga cikin manyan.

Tun a watan Yuni na 2011 ne Ferdinand ya bugawa Ingila wasa da Switzerland da suka tashi 2-2.

Amma kuma aka sake kiransa ya buga wasan da za ta yi da San Marino ranar Juma'a 22 ga watan Maris da kuma na Montenegro ranar Talata 26 ga watan Maris.

Wasannin ne za su tabbatar da kasar da za ta zama ta daya a rukuni na 8, (Group H) na neman zuwa gasar Kofin Duniya.

Karin bayani