Rafael Nadal ya lashe gasar Indian Wells

Rafeal Nadal
Image caption Nadal na fama da guiwarsa ta hagu, wacce wata rana ta yi ciwo wani lokacin kuma da sauki

Zakaran wasan kwallon Tennis din nan, dan kasar Sapaniya Rafael Nadal, ya samu nasarar lashe gasa a karon farko, tun bayan komawarsa fagen wasan tennis.

Dan wasan dai ya je hutun watanni bakwai ne, saboda raunukan da ya samu.

Nadal wanda ciwon guiwa ke damunsa, ya doke abokin karawarsa Juan Martin dan kasar Agentina sau uku a jere.

Inda aka kammala zagayen karshe na gasar ta Indian Wells Masters, da ci 4-6, 6-3, 6-4 a Califonia.

Nadal mai shekaru 26 ya ce yayi matukar farin ciki da nasarar da ya samu, tun bayan komawarsa fagen wasan tennis a watan jiya.