Sneijder ya gargadi Real Madrid

sneijder da drogba
Image caption Sneijder da Drogba za su fuskaci tsohon kocinsu a Madrid

Dan wasan Galatasaray Wesley Sneijder ya ce kwallon da ya ci a nasarar da suka yi 3-1 a wasansu da Kayserispor sako ne ga Real Madrid kafin karawarsu ta wasan gab da na kusa da karshe na Zakarun Turai.

Dan wasan wanda ya bugawa Madrid wasa tsakanin 2007 da 2009 ya ci kwallon ne a lokacin kocin Madrid Jose Mourinho wanda ya horad da shi a Inter Milan ya je kallon wasan.

Dan wasan dan kasar Holland mai shekara 28 ya ce cin wannan kwallo sako ne ga Real Madrid cewa su yi hankali da wannnan haduwa.

A kan Mourinho Sneijder ya ce ''ban gan shi ba tsawon lokaci.

Ina farin cikin sake ganin tsohon malami na a karon farko tun bayan wasan karshe da Bayern.''

Shi ma tsohon dan wasan Mourinho Didier Drogba ya buga wa Galasaray wasa a lokacin da Mourinhon ya je kallon.

Amma kuma ba bu tabbacin tsohon dan wasan tsakiya na Madrid Hamit Altintop zai buga wasan Zakarun Turan saboda ya yi rauni a lokacin wasan da Kayserispor.