Lamouchi : ban yi watsi da Drogba ba

didier drogba
Image caption An fitar da Didier Drogba daga tawagar 'yan wasan Ivory Coast

Kociyan Ivory Coast Sabri Lamouchi ya ce har yanzu Didier Drogba yana da rawar da zai taka a kungiyar wasan kasar.

Kocin ya bayyana hakan ne duk da cewa bai sa dan wasan ba cikin tawagar da zata yi wasan neman shiga gasar Kofin Duniya da Gambia a karshen makonnan ba.

Lamouchi ya ce ba wai ya fitar da Drogba daga tawagar 'yan wasan Ivory Coast ba ne illa dai yana son dan wasan ya yi kokarin dawowa da kwarewa da kuzarinsa.

Ya ce zuwan Drogba China wanda yanzu ya ke kungiyar Galatasaray ta Turkiyya ya samu koma baya a wasansa.