Ferdinand ya fice daga tawagar Ingila

Rio Ferdinand
Image caption Hodgson ya ce ficewar Ferdinanad ba wai yana nufin nan gaba ba zai bugawa kulob din wasa ba

Dan wasan baya na kulob din Manchester United, Rio Ferdinand ya fice daga cikin tawagar Ingila, wacce za ta buga wasannin cancantar shiga gasar cin kofin kwallo na duniya.

Fedinand ba zai shiga wasannin da Ingila za ta buga da San Marino da kuma Montenegro ba.

An cimma hakan ne bayan wata ganawar da aka yi tsakainin dan wasan da kuma manajan 'yan wasan Ingila, Roy Hodgson a ranar Lahadi.

A wajen ganawar dai dan wasan ya ce yana so ya cigaba da takawa Ingila leda.

"Ban ji dadi ba cewa Rio ba zai samu buga wasannin ba, saboda bayanai da suka shafi lafiyarsa, wanda kuma dole ya yi aiki da su. " A cewar Hodgson.

Ferdinand ya yi suka ga tsofaffin 'yan wasan Ingila, wadanda su ka yi hasashen cewa janyewar ta shi, na nuna kawo karshen wasanninsa na kasa da kasa.

Inda ya ce "Na dauka wadannan tsofaffin 'yan wasan da suka sha fama da samun raunuka za su fi kowa sanin abin da ke faruwa, maimakon yin zantuka marasa tushe kamar yadda suke yi."