Tiger Woods ya yi sabuwar budurwa

tiger woods da  lindsey vonn
Image caption Tiger Woods da Lindsey Vonn ''alakarmu ta fara ne daga abokantaka''

Tsohon zakaran wasan golf na duniya Tiger Woods da Lindsey Vonn 'yar Amurkan da ta samu lambar zinariya ta wasan sulun kankara na Olympics sun bayyana cewa suna neman junansu.

'Yan wasan sun sanar da hakan ne ta shafinsu na intanet na Facebook inda suka sanya wani hotonsu da suka dauka tare.

Sanarwar ta zo ne bayan makwannin da aka yi ana rade radin dangantakar tasu.

Ana daukar Ms Vonn mai shekara 28 a matsayin daya daga cikin kwararrun 'yan wasan sulun kankara na zamaninta wadda ta samu lambar zinariya a wasan Olympics na lokacin huturu na 2010 da wasu wasannin da dama.

A da Tiger Woods yana auren Elin Nordegren mai tallata kayan kawa na zamani 'yar kasar Sweden wadda suka rabu a 2010 bayan ya bayyana cewa yana neman wasu matan a waje.

Woods mai shekara 37 tuni ya fara farfado da bajintarsa a fagen wasan na golf wanda ya mamaye tsawon shekaru 10 bayan koma bayan da ya samu sakamakon matsalar auren nasa.

Karin bayani