Beckam ya fara aikinsa na China

david beckam
Image caption David Beckam yace ''baruwana da abin da ya faru a baya.''

Tsohon kyaftin din Ingila David Beckam ya fara aikinsa na Jakadan China na kwallon kafa inda zai rinka ziyartar kungiyoyin wasa da halartar wasanni a kasar domin bunkasa wasan a tsakanin yara.

A farkon watannan ne China ta bashi wannan mukami yayin da kasar ke kokarin dawo da martabar wasan bayan bankado ta'adar rashawa da cuwa-cuwa da aka yi a harkokin wasan a kasar.

Abin da ya kai ga daure 'yan wasa da alkalan wasa da jami'ai da kuma haramtawa wasunsu shiga harkokin wasan kwallon kafar har karshen rayuwarsu.

Beckam mai shekara 37 zai hada aikin ne da kuma bugawa kungiyarsa ta Paris St-Germain ta Faransa wasa.