Kociyoyi sun koka da kora a Ingila

kociyoyi
Image caption Korar kociyoyi ta yi yawa a bana

Kungiyar masu horadda 'yan wasan klub-klub ta Ingila ta koka da yadda kungiyoyin wasa ke korar kociyoyi daga aiki a bana da cewa abin kunya ne.

Shugaban kungiyar Richard Bevan ya ce lamarin a kakar wasannin nan ya zarta na shekaru biyar da suka gabata bayan da kungiyar Blackburn ta sallami kociyanta Micheal Appleton ranar Talata.

Appleton shi ne kociya na uku da Blackburn ta kora a bana bayan Steve Kean a watan Satumba da Henning Berg a watan Disamba.

A kakar wasannin ta 2012-13 kociyoyi 103 ne suka rasa aikinsu ta hanyar sallama ko ajiye aiki a kungiyoyin kwallon kafa na Ingila.

A kan hakan Bevan ya ce ''abin kunya ne ga harkar wasan ganin cewa dukkanin korar an yi ne ba bisa adalci ba kuma hakan na kawo nakasu ga sana'ar.''

A kakar wasannin ta bana ne aka sallami kociyoyin kungiyoyin Premier hudu Roberto Di matteo na Chelsea da Brian McDermott na Reading da Nigel Adkins na Southampton da kuma Mark Hughes na QPR.

Shugaban kungiyar kociyoyin na Ingila Richard Bevan ya ce wajibi ne dukkanin kungiyoyin da ke da nasaba da wasan kwallon kafar su yi aiki tare su tabbatar cewa suna da horon da ya dace da kuma sanin yadda ya kamata a rika tafiyar da harkokin wasan.

Karin bayani