Mourinho ne na daya a yawan albashi

jose mourinho
Image caption Jose Mourinho yana samun dala miliyan 18 a shekara

Kociyan Real Madrid Jose Mourinho ya zama mai horadda 'yan wasan da ya fi daukar albashi mai yawa a duniya.

Kocin dan kasar Portugal bisa binciken wata mujullar wasan kwallon kafa ta Faransa yana samun dala miliyan 18 a shekara.

Carlo Ancelloti na kungiyar Paris St -Germain shi ne ke bi masa baya da dala miliyan 15.5 yayin da kociyan kungiyar Guangzhou ta China shi ma dan Italiya Marcello Lippi ya ke zaman na uku da sama da dala miliyan 14.

Gus Hiddink wanda ke koyar da klub din Anzhi Makhacakala na Rasha shi ne a matsayi na 4 da dala mliyan 14.

Tsohon kociyan Liverpool Kenny Dalglish shi ke bi masa baya a matsayi na biyar inda ya ke samun dala miliyan13 a shekara.

Arsene Wenger na Arsenal da kociyan kasar Rasha Fabio Capello suna matsayi na 6 ne inda suke samun dala miliyan 11 a shekara.

Sir Alex Ferguson na Manchester United da Roberto Mancini na Man City da kuma kociyan kasar China dukkanninsu suna matsayi daya da dala miliyan 7.

Mourinho ya soki FIFA

Haka kuma kociyan na Real Madrid Jose Mourinho ya zargi Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA da yin magudi wajen zaben kociyan kasar Spaniya Vincente del Bosque a matsayin kocin duniya na 2012.

Mourinho ya ce anyi magudi inda aka karkatar da kuri'un wasu masu zabe a lokacin da aka gudanar da zaben wanda aka yi bikin bada lambarsa a watan Janairu.

Kocin wanda yake yi wa kansa lakabin na musamman ya ce ya ki halartar bikin na FIFA ne saboda ya samu labarin magudin da aka yi.

Karin bayani