Ghana na matukar bukatar nasara - Muntari

sulley muntari
Image caption Sulley Muntari ''matasan 'yan wasanmu na wasa a manyan lig-lig na Turai ba na jin zasu wahala''

Dan wasan kasar Ghana na tsakiya Sulley Muntari ya bayyana cewa suna fafutukar ganin sun manta da rashin nasarar da suka yi a gasar Kofin Afrika.

Sannan kuma su yi galaba a kan sudan a wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya da za su yi ranar Lahadi.

Ghana ta sha kashi ne a hannun Burkina Faso a wasan kusa da na karshe a Afrika ta Kudu kuma dan wasan wanda bai samu damar zuwa gasar ba yana fatan zuwa gasar Kofin Duniya a Brazil.

Muntari mai shekaru 28 wanda ya ce sun zaku su ga sun yi nasarar zuwa gasar ta duniya ya kara da cewa ''wasan da za mu yi da Sudan ba zai kasance da sauki ba amma muna son yin nasara ta ko wana hali.''

Game da rashin nasarar ta Ghana a gasar Kofin Afrika wasu sun yi ta sukan lamirin kociyan kasar Kwesi Appiah saboda amfani da yai da matasan 'yan wasa.

Maimakon fitattun 'yan wasan kasar irin su tsohon kyaftin din su John Mensah da dan wasan Marseille Jordan Ayew, yayin da daman tun da farko ya fitar da Andre Ayew daga tawagar.

Duk da haka yanzu ma kocin ya cigaba da tsarinsa na amfani da matasan 'yan wasan inda a wannan karon ya gayyato wadansu sababbi 4 da suka hada da dan wasan Arsenal dake zaman aro a Fulham Emmanuel Frimpong a wasan da Ghanan za ta yi da Sudan ranar Lahadi.

Muntari yana ganin matasan 'yan wasan za su fitar da kasar kunya da za su wuce Zambia ta daya a rukuninsu na hudu (Group D) wadda ta yi musu tazara da maki 3 inda za su fara da nasara a kan Sudan ta uku a rukunin.