Tennis : Sharapova ta yi nasara a Miami

maria sharapova
Image caption Maria Sharapova ka iya komawa matsayi na daya a duniya

Ta uku a jerin gwanayen wasan tennis a duniya Maria Sharapova ta samu nasarar zuwa zagayen 'yan 16 a gasar Miami Masters.

Sharapova mai shekara 25 wadda sau hudu ta na daukar Kofunan manyan gasanni ta samu nasarar ce inda ta yi waje da Elena Vesnina ita ma 'yar Rasha da maki 6-5 6-2.

Sharapova wadda a karshen makon da ya gabata ta dauki kofin gasar Indian Wells yanzu za ta kara da Klara Zakopalova a zagaye na gaba.

Zakopalova ta samu nasara ce a kan Maria Kirilenko 6-2 7-6 kafin ta kai matakin haduwar da Sharapova.

Sharapova ka iya sake karbar matsayinta na da ta daya a duniya daga Serena Williams idan yanayin wasan ya zo mata daidai nan gaba a makon.

Sau hudu Sharapova ta zo ta biyu a gasar Miami Masters.

Serena Williams ta je filin wasan ne ranar Lahadi a kan keke domin gudun jinkiri saboda cuncrundon ababan hawa a hanya.

A wasanta da Ayumi Morita 'yar Japan Serena mai shekaru 31 ta samu nasara da maki 6-3 6-3.

Ita kuwa 'yar uwar Serena Venus mai shekaru 32 ta janye daga gasar ce saboda ciwon baya kafin karawar zagaye na uku da Sloane Stephens ita ma 'yar Amurka.