'Yan wasan Afrika ta Tsakiya sun ki komawa gida

afrika ta tsakiya da afrika ta kudu
Image caption Juyin mulki ya hana 'yan Afrika ta Tsakiya komawa gida

'yan wasan Jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun jinkirta komawarsu gida daga Afrika ta Kudu bayan wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya saboda mamayar da 'yan tawaye suka yi wa babban birnin kasarsu Bangui.

A ranar Lahadi 'yan tawaye suka hambarar da gwamnatin shugaba Francois Bozize suka kama fadar mulkin kasar abinda ya tilasta masa ya tsere.

'yan wasan kasar da suke kungiyoyin kasashen Turai za su tafi Paris ranar Litinin yayin da wadanda suke wasa a cikin gida zasu tafi Doulan Kamaru ranar Talata.

Kungiyar kasar Afrika ta Kudu, Bafana Bafana ta yi nasara a kan su ranar Asabar da ci 2-0 a Cape Town.

Manajan kungiyar William kongo ya ce daman tawagar 'yan wasan ta na komawa gida ne ta bangaren makwabciyarta ta yamma Kamaru, amma a yanzu 'yan wasan za su tsaya a Doula na wasu kwanaki kafin komarsu idan yanayin tsaro ya inganta.

Sai dai kuma Kongo ya ce 'yan wasan gidan su na son komawa gida duk da halin da ake ciki kuma watakila su koma a cikin wannan makon.

Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta kudu ta ce lokaci bai yi ba yanzu da za ta yi wa Hukumar kwallon kafa ta Afrika ko ta duniya Fifa magana kan ko a daga lokacin sake karawar kasashen ta neman shiga gasar Kofin Duniya a Afrika ta Tsakiya a watan Yuni.