Costa Rica ta yi korafin wasanta da Amurka

sepp blatter
Image caption Sepp Blatter : Fifa za ta duba korafin Costa Rica

Costa Rica ta aikawa Hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa takardar korafi game da yanayin filin wasan da Amurka ta kara da ita a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya a Amurkan.

Wasan na ranar Juma'a a Denver an yi shi ne a yanayin filin wasan da kociyan Costa Rica Jorge Luis Pinto ya kira ''abin kunya ga wasan kwallon kafa.''

Costa Rica ta yi rashin nasara a wasan inda Amurka ta yi mata 1-0 abin da ya sa ta zama ta karshe a rukunin karshe na kasashe shida na neman zuwa gasar kofin Duniyar.

Fifa ta ce tana nazarin takardar korafin ta Costa Rica wadda a ciki hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce dusar kankara ta mamaye filin wasan har ta kai ma ba a ganin zanen filin kuma kwallon ba ta tafiya yadda ya kamata.

A ranar Talata kasashen da ke rukunin za su cigaba da fafatawa a tsakaninsu inda Costa Rica za ta hadu da Jamaica, Mexico za ta karbi bakuncin Amurka yayin da Panama da Honduras za su kara.