Golf: Woods ya koma na daya

tiger woods
Image caption Tiger Woods ya dawo na daya a karo na 11

Tsohon zakaran duniya na Golf Tiger Woods ya sake komawa matsayinsa na daya a karon farko tun watan Oktoba na 2010 bayan ya dauki kofin gasar Arnold Palmer.

Woods dan Amurka mai shekaru 37 ya yo kasa daga matsayin na daya zuwa na 58 a watan Nuwamba na 2011.

Yanzu ya sake karbe matsayin na dayan ne daga Rory Mcllroy dan Ireland ta Arewa wanda bai halarci gasar ta Arnold Palmer ba.

Nasarar ta Tiger Woods a filin Bay Hill a Amurka itace ta 77 kuma ta 3 a shekaran nan ta 2013 kuma wannan shi ne karo na 11 da ya ke zama na daya a duniya.

Justin Rose dan Ingila na biyar a jerin gwanayen tennis na duniya shi ya zo na biyu a gasar wanda hakan ya sa ya dawo matsayin na uku a duniya.

Karin bayani