Arsenal ta lallasa Reading da ci 4-1

Arsenal
Image caption Cazorla ya jefa kwallo ta biyu jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci

Arsenal na ci gaba da yunkurinsu na shiga gasar cin kofin zakarun Turai inda suka lallasa Reading da ci 4-1 a gasar Premier ta Ingila.

Gervinho ne ya fara zira kwallo a zagayen farko na wasan kafin Santi Cazorla ya jefa ta biyu jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Cazorla ya nuna kware wa sosai wurin zira kwallo ta biyun kafin Olivier Giroud ya zira ta uku.

Reading sun rage yawan kwallayen ta hannun Hal Robson-Kanu, sai dai Mikel Arteta ya zira wa Arsenal kwallo ta hudu daga bugun fanareti bayan da aka tade Alex Oxlade-Chamberlain.

Wannan nasara ta Arsenal ta sa Reading ta koma matakin karshe a teburin gasar ta Premier.

Ga yadda wasannin wannan makon suka kaya:

Sunderland 0 - 1 Manchester United Arsenal 4 - 1 Reading Manchester City 4 - 0 Newcastle United Southampton 2 - 1 Chelsea Swansea City 1 - 2 Tottenham Hotspur West Ham United 3 - 1 West Bromwich Wigan Athletic 1 - 0 Norwich City

Karin bayani