An rufe filin wasan Olympics a Brazil

Brazil
Image caption Brazil ce za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya da kuma Olympics

An rufe filin wasan da aka tsara za a gudanar da wasan guje-guje a gasar Olympics ta 2016 a Brazil har sai abin da hali ya yi, saboda rashin karkon ginin.

Shekaru shida da suka wuce ne kawai aka gina filin wasan na Joao Havelange a garin Rio de Janeiro.

Ana kuma amfani da shi a matsayin filin wasan kwallon kafa a birnin, a daidai lokacin da ake gyara filin wasa na Maracana saboda gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na badi.

Wannan ba karamin abin kunya ba ne ga Brazil a daidai lokacin da take shirin karbar bakuncin manyan gasar wasanni biyu, a cewar masu aiko da rahotanni.

Mahukunta sun tabbatar da jinkiri a aikin filin wasa na Maracana da kuma matsalar kudi a aikin daya filin wasan.

A nan ne dai ake sa ran za a gudanar da bikin bude gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi badi.

Karin bayani