Aruna Dindane ya koma Crystal Palace

Aruna Dindane
Image caption Aruna Dindane ya taka leda sosai a Ivory Coast

Crystal Palace sun dauki dan wasan gaba na Ivory Coast Aruna Dindane har zuwa karshen kakar bana.

Dan wasan mai shekaru 32, wanda ya taba taka leda a Portsmouth a 2009-10, ba shi da kwantiragi da kowanne kulob bayan da ya bar kungiyar Al-Sailiya Sport Club na kasar Qatar a watan Disamba.

Kocin Palace Ian Holloway, ya fada a shafin internet na kulob din cewa: "Aruna yana horo da mu kuma mun ga abinda muke bukata domin ya kasance tare da mu.

"Na son irin taimakon da zai iya yi mana idan ya samu kansa a yanayin da ya dace."

Dindane ya taka leda sau 67 a Ivory Coast, inda ya zira kwallaye 11 sannan ya halarci gasar cin kofin duniya sau biyu.

Tun bayan da ya bar Portsmouth, inda ya zira kwallaye 10 a wasanni 24, ya taka leda a kungiyoyi uku daban-daban a kasar Qatar.