Kofin FA : Chelsea ta yi waje da Man U

chelsea demba ba
Image caption Demba ba ya sa Man United ta maida hankali kan Premier kawai

Chelsea ta kawo karshen fatan da Manchester United take yi na daukar kofunan Ingila biyu a bana inda ta fitar da ita daga gasar Kofin Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA.

A karawar ta wasan dab da na kusa da karshe da aka yi a Wembley wadda ita ce ta biyu bayan haduwarsu ta farko da suka tashi 2-2 Demba Ba ne ya ci wa Chelsea kwallo daya da ta baiwa kungiyar nasara.

Ba ya ci kwallon ce a minti na 49 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Yanzu wasa daya ya rage Chelsea ta kai ga wasan karshe na kofin FA karo na biyar a shekaru bakwai, inda za ta kara da Manchester City.

Chelsea ta dauki kofin a 2007 da 2009 da 2010 da kuma 2012.

Chelsea za ta kara a wasan kusa da karshe da Manchester City ranar 14 ga watan Aprilu a Wembley.

Duk da wannan nasara kociyan Chelsean Rafeal Benitez ya ce kasance cikin kungiyoyi hudu da ke kan gaba a Premier shi ne burinsa har yanzu.

Karin bayani