Zakarun Turai : PSG ta hana Barca nasara

psg barcelona
Image caption Zlatan Ibrahimovic ya muzguna wa tsohuwar kungiyarsa

Kungiyar Paris Saint-Germain ta Faransa ta hana Barcelona tsira da nasara a gasar Kofin Zakarun Turai.

A karawar da suka yi a gidan PSG wadda ita ce ta farko a wasan dab da na kusa da karshe na gasar sun tashi 2-2.

Messi ne ya fara daga ragar PSG a minti na 38 sannan kuma Ibrahimovic ya rama a minti na 79.

Can a minti na 89 ne kuma Barcelona ta sami fanareti wadda Xavi ya buga kuma ya ci.

Amma kuma ana dab da tashi bayan karin 'yan mintinan da aka bata sai Matuidi ya ramawa PSG kwallo ta biyu a kusan minti na 94.

A ranar 10 ga watan Aprilu ne za a yi karawa ta biyu inda Paris Saint-Germain za ta je gidan Barcelona wadda ta ke da galaba a karawar farkon ta kwallaye 2 da ta ci a gidan PSG.

Bayern Munich da Juventus

A daya wasan da aka yi na Zakarun Turan tsakanin Bayern Munich da uventus ta Italiya zakarun Jamus din a gidansu sun yi galaba a kan zaakarun Italiyan 2-0.

Blaise Alaba ne ya fara jefa kwallo a ragar bakin kasa da minti daya da fara wasan sannan kuma Mueller ya biyo baya da ta biyu a minti na 63.

Zakarun Italiyan Juventus yanzu suna da jan aiki a gabansu wajen rama kwallayen biyu a karawa ta biyu da za a yi a gidansu a mako mai zuwa ranar 10 ga watan Aprilu.

Ana ganin hakan ne saboda yadda suka kasa tabuka wani abin a-zo-a-gani a wasan nasu.

A ranar Laraba 3 ga watan Aprilu ne kuma za kara a kashi na biyu na gasar Zaakarun Turan

Malaga za ta hadu da Borussia Dortmund yayin da Real Madrid zata kara da Galatasaray.