Zakarun Turai : Real Madrid ta yi sa'a

real madrid galatasaray
Image caption Real Madrid na neman kofin Zakarun Turai na 10

Real Madrid ta lallasa Galatasaray 3-0 a wasan dab da na kusa da karshe na Kofin Zakarun Turai karawar farko.

Cristiano Ronaldo ne ya fara jefa kwallo ragar kungiyar ta Turkiyya a minti 9 da wasa.

Karim Benzema shima ya biyo baya da kwallo ta biyu a minti na 29 a ragar bakin.

Didier Drogba da Emmanuel Eboue sun barar da damammakin da Galatasaray ta samu na cin kwallaye.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma sai Higuain wanda ya maye gurbin Benzema ya jefa kwallo ta uku saura minti 17 wa'adin wasan ya cika.

Nasarar ta baiwa Real Madrid damar zuwa Turkiyya karawa ta biyu ranar 9 ga watan Aprilu hankali kwance ganin ba a sa mata kwallo ko da daya a raga ba.

Ita kuwa Galatasaray tana da gagarumin aiki a gabanta na rama kwallayen uku.

Real Madrid na harin zuwa wasan kusa da na karshe a karo na 24 kuma tana neman kofin Zakarun Turan na goma.

Malaga da Borussia Dortmund

A daya wasan na Zakarun Turan da aka yi tsakanin Malaga ta Spaniya da zakarun Jamus Borussia Dortmund sun tashi 0-0.

Mario Gotze da Robert Lewandowski sun barar da damar da Dortmund ta samu a lokuta dabam-dabam.

Karawa ta biyu za a yi ta ne a Jamus ranar 9 ga watan Aprilu.

Karin bayani