Odemwingie na magana sakaka - Siasia

Peter Osaze Odemwingie
Image caption Siasia ya taba horar da Odemwingie a gasar Olympics na shekarar 2008

Tsohon mai horar da 'yan wasan Najeriya, Samsong Siasia ya bayyana dan wasan Najeriya, wanda ke taka wa West Brom leda, Peter Odemwinge da cewa mutum ne dake magana sakaka.

Kuma a cewar Siasia akwai bukatar dan wasan ya nutsu.

Odemwingie mai shekaru 31 a duniya bai samu shiga tawagar Najeriya da ta dauki kofin zakarun nahiyar ba, saboda rashin jituwa tsakaninsa da Stephen Keshi.

Siasia wanda ya taba aiki tare Odemwingie a kasashen ketare yace, matakin da Keshi ya dauka na kin sanya dan wasan cikin tawagar ya yi daidai.

"Mutum ne mai magana sakaka, kuma ko da ni ne ke horar da 'yan wasan Najeriya ba zan sanya Odemwinge a cikin tawagar ba" Inji Siasia.

Samsong wanda ya jagoranci kungiyar 'yan wasan Najeriyar daga shekarar 2010 zuwa 2011 ya kara da cewa "Muna bukatar 'yan wasan da za su shige gaba su zama jagora na gari ga 'yan baya, idan bai yi hakan ba to zai zamo wake daya bata gari"

A kulob dinsa dai Odemwingie ya samu cigaba da aiki yadda manajan kulob dinsa ya ke so, bayan yunkurinsa na komawa QPR bai yi nasara ba.

Sai dai Siasia har yanzu yana da shakku game da dan wasan "Akwai bukatar ya samu nutsu wa, ya san a yanzu yana da iyali da za su dinga dubansa a matsayin abin koyi."

"Ina fatan hankali zai zo masa cinkin gaggawa, domin 'yan Najeriya za su so ya dawo cikin tawagar kasar." Inji tsohon kocin.