Pacquiao zai sake karawa da Marquez.

pacquiao marquez
Image caption Manny Pacquiao na neman ramuwar gayya a kan Juan Manuel Marquez.

Tsohon zakaren damben boksin na matsakaita na duniya Manny Pacquiao ya shirya sake tarar mutumin da ya buge shi a watan Disamba.

Mai magana da yawun tsohon zakaran na WBO ya ce ana nan ana tattaunawa game da sake karawar tasa da Juan Manuel Marquez a cikin watan Satumba.

A watan Yuni dan damben ya rasa kambunsa na WBO ga Timothy Bradley dan Amurka a wani hukunci mai sarkakiya.

Sannan kuma a watan Disamba Marquez ya yi galaba a kansa da bugun kwab daya a karawarsu.

Shi dai Pacquiao mai shekaru 34 bayan sana'ar damben dan siyasa ne da a yanzu yake neman a sake zabensa a matsayin dan majalisa a zaben tsakiyar wa'adi na kasarsa Philippines a wata mai zuwa.

Karin bayani