An yankewa Carlos Tevez hukunci

carlos tevez
Image caption Carlos Tevez ba shi da lasisin tukin mota na Birtaniya

Dan wasan manchester City Carlos tevez ya amsa laifin cewa ya saba dokar hana shi tukin mota a Ingila.

A kan hakan alkalin kotun majistaren da aka gurfanar da shi gabansa ya yanke masa hukuncin aikin gwale-gwale na yiwa al'umma hidima na tsawon sa'oi 250.

Baya ga wannan kuma alkalin ya haramta masa tukin mota tsawon watanni 6 da tarar fam 1000.

An dai kama Carlos Tevez ne dan Argentina bisa laifin saba hukuncin da aka yi masa a baya na hana shi tuki saboda kin amsa wasikar da 'yan sanda suka aika masa kan tuhumar laifin gudun da ya wuce ka'ida da mota.

Karin bayani