Armstrong ya fasa komawa wasan ninkaya

lance armstrong
Image caption Lance Armstrong ya amsa cewa yayi amfani da kwayoyi a hirarsa da Oprah Winfrey

Dan tseren keken nan na Amurka da aka haramtawa tseren har tsawon rayuwarsa saboda amfani da kwayoyin kara kuzari Lance Armstrong ya janye aniyarsa ta komawa wasan ninkaya.

Armstrong mai shekara 41 wanda aka karbe wa lambobin da ya ci na tseren duniya na Faransa bakwai bayan yaki kare tuhumar da aka yi masa ta amfani da kwayoyin a watan Agusta a da ya ce zai shiga gasar ninkaya a Texas a karshen makon nan.

Damar da ya ke da ita ta shiga gasar linkayar ta Amurka bata shafi ka'idojin hukumar yaki da ta'ammali da kwayoyin kara kuzari ta Amurka ko ta Duniya ba.

Amma hukumar wasan ninkaya ta duniya ta ce ba ta yarda ya shigo wasanta ba.

Da dai Armstrong zai shiga gasar ta tazarar yadi 500 da ta yadi 1000 da kuma ta 1, 650 a garinsa na Austin.

Karin bayani