Yobo ya soki Keshi

joseph yobo
Image caption Joseph Yobo sau 95 yana bugawa Najeriya wasa

Kyaftin din 'yan wasan Najeriya na kwallon kafa Joseph Yobo ya shiga sahun masu cacar-baki da kociyan kasar Stephen Keshi.

Joseph Yobo mai shekaru 32 shi ne yafi kowana dan wasa bugawa Najeriya wasanni.

A tarihi sau 95 yana yi wa kasar wasa.

Dan wasan na kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya ya ce kin gayyatarsa wasan Najeriya da Kenya na neman zuwa gasar Kofin Duniya da kuma kin sanar da shi rashin kiransa cin mutunci ne gareshi.

Dan wasan West Bromwhich Peter Odimwingie da Emmanuel Emenike na Spartak ta Moscow sun dade suna cacar-baki da Keshi.