Fifa ta daga wasannin rukunin Najeriya

steven keshi
Image caption Najeriya ce kan gaba a rukuninta

Hukumar kwallon kafa ta Duniya ta amince da bukatar Najeriya ta sauya ranakun wasanninta 2 na neman zuwa gasar Kofin Duniya a watan Yuni.

Bayan da Fifa ta sauya mata ranakun neman zuwa gasar Kofin Duniyar kafin gasar Zakarun nahiyoyi a watan Yuni, hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta kuma bukaci a daga ranakun sauran wasannin rukunin su dace da nata.

A kan hakan Fifa yanzu ta matsar da ranakun dukkanin wasannin rukunin su kasance daya wato 5 ga watan Yuni da kuma 12 ga watan Yuni.

Najeriya ta bukaci hakan ne saboda tana ganin takwarorinta na rukunin ka iya samun dama fiye da ita idan ba a daidaita lokutan ba saboda ita da malawi kowacce nada maki 5-5.

Saboda haka idan Najeriya ta yi wasa kwanaki biyu kafin Malawi ta yi hakan zai sa Malawin ta san matsayinta da kuma abin da ya kamata ta yi ta wuce Najeria.

Najeriya ce ta daya a rukuninsu na neman zuwa gasar Kofin Duniya, ita da Malawi kowacce da maki biyar-biyar amma Najeriya na gaba da bambancin kwallaye.

Daga ranakun wasannin ya baiwa Najeriya zakarun Afrika damar zuwa gasar zakarun nahiyoyi da za a yi a Brazil.

Gasar wadda za a fara ranar 15 ga watan Yuni ta kunshi zakarun Duniya Spaniya da Brazil zakarun gasar sau 6.