Premier : Chelsea ta casa Sunderland

fernando torres
Image caption Shigowar Fernando Torres wasan ta taimaka wa Chelsea

Sabon kociyan Sunderland Paolo Di Canio ya soma aikinsa da rashin sa'a a hannun Chelsea da ci 2-1.

Di Canio dan kasar Italiya da farkon wasan ya samu yadda yake so.

A lokacin da dan wasan Chelsea Cesar Azpilicueta ya ci kansu a minti na 45 kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo ne kuma a minti na 47 Matt Kilgallon na Sunderland shi ma ya ci kansu.

Chelsea ta sami kwallonta ta biyu da ta bata nasara a kan Sunderland a minti na 55.

David Luiz ne na Chelsean ya bugo kwallo amma ta taba Branislav Ivanovic shi ma na Chelsean ta fada ragar Sunderland.

Duk da galabar da Chelsea ta yi a kanta Sunderland ta na matsayi na 17 da maki 31 ba ta fada cikin kungiyoyi 3 dake hadarin faduwa daga Premier ba.

Sai dai ta zarta Wigan ta 18 ne da bambancin kwallaye kawai.

Chelsea kuma ta na matsayi na uku da maki 58.