Zakarun Afrika : Zamalek ta yi gaba

zamalek caf
Image caption Zamalek Zakarun Afrika sau 5

Zamalek ta Masar ta sami shiga zagayen fitar da kungiyoyi na karshe 16 na gasar Kofin Zakarun Afrika na kwallon kafa.

Ta sami nasarar ce bayan sun tashi ba ci tsakaninta ta tsoffin zakarun gasar Vita ta Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo.

A karawar farko a Alkahira sun tashi Zamalek na da ci 1 vita din kuma 0.

Mai rike da kofin Al Ahly ita ma ta sami zuwa matakin na gababayan ta ci Tusker ta Kenya 2-0 wasa gida da waje 4-1.

Tsoffin zakarun gasar Esperence na Tunisia da Orlando Pirates na Afrika ta Kudu da Recreativo Libolo na Angola da kuma Stade Malien na Mali sun wuce gaba.

Sai dai kuma anyi waje da Asante Kotoko ta Ghana. A wasan da suka yi a Kumasi zakarun gasar na 1970 da 1983 sun tashi 1-1 da JSM Bejaia ta Algeria bayan a karawr farko sun tashi 0-0.

Kwallon da JSM ta sanya a gidan 'yan Asanten ta ba sa suka sami galaba a kan kungiyar ta Ghana.

Esperence wadda sau day ta taba daukar kofin kuma ta zo ta biyu sau biyu ta sami nasarar ce bayan ta ci bakinta Primeiro Agosto ta Angola 1-0 kamar yadda ta bi ta gida ta yi galaba a kanta a karawar farko.

Pirates ta Afrika ta Kudu wadda ita kadai ta taba daukar kofin a kasar ta fitar da Zanaco ta Zambia 2-1 a Soweto bayan a farkon haduwarsu sun tashi 1-0.

Libolo ta Angola ta sami nasara a kan El Merreikh 2-1 a Sudan, jumulla wasa gida da waje4-2. Haka ita ma Al Hilal ta yi waje daga gasar duk da ta yi nasara a Sudan a kan bakinta Sewe San Pedro 3-1. A karawar farko ta sha kashi 4-1 a Ivory Coast.

Stade Malien ta yi galaba a kan Casa Sport ta Senegal 2-0 a Bamako bayan ta yi nasara a kan bakin nata 2-1 da farko.

Entente Setif ta Algeria ta fitar da ASFA Yennenge ta Burkina Faso 5-4 gida da waje.