Man City ta doke Man United

manchester united manchester city
Image caption Manchester City ta bi United har gida ta casa ta

Manchester City ta rage tazarar da Man United ta bata a Premier zuwa maki 12 bayan da tayi nasara a kanta a Old Trafford 2-1.

James Milner ne ya fara sanay bakin gaba bayan hutun rabin lokaci a minti na 51.

Manchester United ta rama bayan da Robin van Persie ya yi wani bugun tazara da kwallon ta taba kyaftin din City Vincent Kompany ta shiga raga, ya ci kansu.

Sergio Aguero wanda ya yi canjin Samir Nasri ne ya jefa kwallo ta biyu da ta baiwa Manchester City nasara minti 12 kafin cikar wa'adin wasan.

Karawar ta abokanan hamayyar na Manchester ta kai ga alkalin wasa ya baiwa 'yan wasa 8 katin gargadi.

Wannan shi ne karon farko da Manchester United ta yi rashin nasara a wasanni 18 na Premier a bana.

Manchester United tana matsayin ta daya da maki 77 ita kuma Manchester City tana bi mata da maki 65 yayin da ya rage wasanni 7 a kammala gasar ta bana.

Kuma United din tana kan hanyar daukan kofin ne a karo na 20.

Karin bayani