Zakarun 2013 : Woods zai hadu da Donald

masters 2013 woods da donald
Image caption Woods da Donald za su fafata a Gasar Zakaru ta 2013

Zakaran wasan Golf na duniya Tiger Woods zai hadu da Luke Donald na Ingila a gasar Zakarun Golf ta 2013.

Woods wanda sau hudu yana daukar kofin gasar zai hadu da Donald a zagaye biyu na bude gasar da za a yi a Georgia daga 11 zuwa 14 ga watan Aprilu.

Shi kuwa Rory Mcllroy tsohon zakara kuma na biyu a fagen wasan na duniya an hada shi a rukuni daya da Keegan Bradley zakaran gasar kwararrun Golf na Amurka ta 2011, da kuma Freddie Jacobson na Sweden.

Zakaran gasar na bara Bubba Watson shi kuwa yana rukuni daya ne da zakaran kofin Ryder na Turai Ian Poulter.

Lee Westwood na Ingila zai hadu ne da Jim Furyk zakaran US Open na 2003

A ranar Alhamis Sandy Lyle wanda ya dauki kofin gasar ta Zakarun Golf a 1988 zai fara wasansa.

Phil Mickelson na Amurka zakaran gasar sau uku zai hadu da tsohon na daya a wasan Martin Kymer dan Jamus da kuma Louis Oosthuizen wanda ya zo na biyu a gasar bara.

Karin bayani