Mikel bai damu da Kofin Europa ba

mikel obi
Image caption Mikel Obi ya ce ''mun fi sabawa da gasar Zakarun Turai''

Dan wasan Chelsea John Milkel Obi ya ce ya zaku su sami damar shiga gasar kofin Zakarun Turai a bana.

Kungiyar Chelsea ta sami cancantar zuwa matakin wasan dab da na kusa da karshe na Kofin Europa bayan an fitar da ita daga gasar zakarun Turai.

Dan wasan mai shekaru 25 ya ce gasar Zakarun Turai aka fi sanin kungiyar da ita kuma abin da 'yan wasan ke son ganin sun samu ke nan.

Ya ce ba wai sun raina gasar Kofin Europa ba amma dai ta Zaakarun Turai ta fi armashi.

Dan wasan na Najeriya ya kara da cewa ''abin takaici ne ka ga ana wasan Zakarun Turai amma kai sai na Europa ka ke yi.''

Karin bayani