Real Madrid ta tsira a hannun Galatasaray

cristiano ronaldo
Image caption Ronaldo ya tserar da Real Madrid

Real Madrid ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai.

Kungiyar ta Spaniya ta sami damar ce bayan ta tsira a hannun Galatasaray ta Turkiyya da ci 5-3 wasa gida da waje na dab da na kusa da karshe.

A karawar da suka yi a makon da ya wuce a Spaniya Real Madrid ta ci 3-0.

A fafatawarsu ta biyu ranar Talatar nan Galatasaray ta ci Real 3-2.

Ronaldo ne ya fara saka kwallo a ragar Galatasaray a minti 8 na wasan.

Emmanuel Eboue ya rama kwallon a minti na 57 kafin Sneijder ya kara ta biyu a minti na 71 sannan kuma Drogba ya kara ta uku saura minti 18 lokaci ya cika.

Sai dai kuma bayan cikar wa'adin minti 90 na wasan ne kuma Ronaldo ya kara kwallon Madrid ta biyu.

Borussia Dortmund da Malaga

Borussia Dortmund ita ma ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe bayan ta tashi da Malaga 3-2 a Jamus.

A karawarsu ta farko a Spaniya sun tashi canjaras 0-0.

A wasan na Talata Joaquin ne ya fara ci wa Malaga kwallonta cikin minti 25 da wasa kafin Lewandowski ya rama wa kungiyar ta Jamus a minti na 40.

Eliseu ya kara jefa kwallo ta biyu ragar 'yan Dortmund da ake ganin za ta baiwa bakin damar nasara.

Amma a mintinan karshe na karin lokaci Reus da Felipe Santana suka ci kwallaye biyu da Borussia ta sami nasara.

Karin bayani