Bayern Munich a wasan kusa da karshe

bayern munich da juventus
Image caption Bayern Munich ta lallasa Juventus gida da waje

Bayern Munich ta kai wasan kusa da karshe na Zakarun Turai karo na uku a shekaru hudu.

A wannan karon zakarun na Jamus sun kai matakin ne bayan sun yi nasara a kan zakarun Italiya Juventus 4-0 wasa gida da waje.

A wasansu na farko a Jamus Bayern sun ci Juventus 2-0, sannan kuma yanzu sun sake galaba a kansu da 2-0 a Italiya.

Mario Mandzukic ne ya ci kwallon farko bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 60.

Claudio Pizzaro ne ya kara ta biyu dab da tashi daga wasan a minti na casa'in.

A ranar Juma'a za a fasalta yadda kungiyoyin da suka shiga wasan kusa da karshen za su hadu.