Europa : Chelsea ta tsira

  • 11 Aprilu 2013
chelsea rubin kazan
Image caption Chelsea ta kai wasan kusa da karshe na Europa bayan galaba a kan Rubin Kazan

Kungiyar Chelsea ta zama ta farko da ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe na gasar Europa.

Kungiyar ta tsallake rijiya da baya duk da nasarar da 'yan Rubin Kazan suka samu a kanta 3-2 a karawar da suka yi a Rasha. Chelsea ce ke kan gaba a wasan bayan a karawar farko ta ci Rubin din 3- 1.

Fernando Torres ne ya fara ci wa Chelsean kwallonta minti biyar da shiga fili

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 51 Marcano ya rama wa masu masaukin baki.

Sai dai kuma minti 4 tsakani ne kuma sai Victor Moses ya ci wa Chelsea kwallo ta biyu mai zaman 'ya'ya biyu.

Gokdeniz Karadeniz na Rubin Kazan shi ne ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar Chelsean can aminti na 62, kafin kuma a minti na 75 Bebras Natcho ya ci wa 'yan Rashan kwallo ta 3 da bugun fanareti