Sakamakon wasannin Europa

fc basel da tottenham
Image caption FC Basel ta fitar da Tottenham ta je wasan kusa da karshe na Europa a karon farko

Fatan Tottenham a gasar Kofin Europa na bana ya kawo karshe bayan da FC Basel ta fitar da ita da bugun fanareti.

An kai ga fanaretin ne bayan karshen wa'adin wasan na mintuna 90 da kuma lokacin fitar da gwani na karin mintina 30.

Kungiyar ta Switzerland ta yi nasara ne da ci 4-1 a bugun fanaretin bayan sun tashi 2-2 jumulla 4-4 a karawarsu biyu.

Clint Dempsey ne ya fara ci wa Tottenham kwallont a minti na 23 kafin Mohamed Salah ya rama minti 4 tsakani.

Aleksander Dragovic ya jefa kwallo ta biyu ragar Tottenham a minti na 49, sannan kuma a minti na 82 Dempsey ya sake ci wa Chelsea ta biyu.

A karon farko FC Basel yanzu ta sami zuwa wasan kusa da na karshe na Europa.

Newcastle da Benfica

Ita ma kungiyar Newcastle ta yi waje daga gasar ta Europa bayan sun tashi 1-1 da Benfica a karawarsu ta biyu a gidan Newcastle.

A karawar farko a gidan Benfica an ci Newcastle 3-1, sakamakon wasan gaba daya ya kasance 4-2 jumulla.

Fenerbahce da Lazio

Kungiyar Fenerbahce ta sami nasarar zuwa wasan kusa da na karshen bayan ta yi galaba a kan Lazio da ci 2-0 a karawar da suka yi ranar Alhamis din na.

A wasan farko da aka yi a gidan Lazio sun tashi 1-1, jumulla wasanni biyun ke nan sakamakon ya kasance Fenerbahce ta yi nasara da ci 3-1.

A ranar Juma'a ce za a fitar da tsarin yadda kungiyoyin da suka kai wasan kusa da karshen za su hadu.